Isa ga babban shafi

Rukunin farko na dakarun MDD sun fara ficewa daga Jamhuriyar Congo

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun fara ficewa daga jamhuriyyar demoradiyyar Congo a jiya Laraba, tare da mika sansaninsu ga ‘yan sandan kasar, matakin da ke zuwa a dai dai lokacin da shugaba Felix Tshisekedi ke shirin ganawa da takwaransa na Rwanda Paul Kagame don tattaunawa game da rikicin da ke tsakaninsu na zargin Kigali da hannu a matsalolin tsaron Kinshasa.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato Monusco yayin wani aikin sintiri a yankin Munigi mai tazarar kilomita 8 daga Goma da ke gabashin Congo, ranar 19 ga watan yuli, 2013.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato Monusco yayin wani aikin sintiri a yankin Munigi mai tazarar kilomita 8 daga Goma da ke gabashin Congo, ranar 19 ga watan yuli, 2013. © AFP
Talla

Yayin wani bikin ficewar dakarun bayan kawo karshen aikinsu a Congon da ya gudana a sansanin Kamanyola da ke gab da iyakar kasashen Rwanda da Burundi anga yadda aka sauke tutocin Majalisar Dinkin Duniya da na Pakistan dama sauran kasashen da dakarunsu ke cikin MONUSCO tare da mika sansanin ga ‘yansandan kasar tun a jiya Laraba.

Tun farko Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da kanta ta bukaci ficewar dakarun na Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka fara aiki tun daga shekarar 1999 bayan da ta yi zargin cewa suke yiwa tsaronta zagon kasa ta hanyar taimakawa kungiyoyi masu rike da makamai maimaikon aikin da aka girkesu domin yi wajen bai wa fararen hula kariya da kuma kange kasar daga barazanar tsaro.

Akwai dai dakarun na Majalisar Dinkin Duniya akalla dubu 13 da 500 a Congo ciki har da ‘yan sanda dubu 2 wadanda aka karkasa zuwa sassan kasar 3 da suka kunshi Ituri da arewaci da kudancin Kivu wadanda ke da sansanoni akalla 14 da za su mika su ga jami’an tsaron kasar.

Rahotanni sun ce dakarun za su shafe daga yanzu har zuwa watan Afrilu suna ficewa daga Congo, yayinda fararen hular cikin rundunar ta MONUSCO za su kammala ficewa a watan Yunin shekarar nan.

A bangare guda yayin wata ziyarar shugaban na Congo Felix Tshisekedi a Angola ya shaidawa shugaba Joao Lourenco cewa a shirye ya ke ya gana da takwaransa na Rwanda Paul Kagame don tattaunawa kan matsalolin tsaron da ke ci gaba da ta’azzara a gabashin Congo ganawar da bayanai ke cewa za ta gudana bisa shiga tsakanin Lourenco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.