Isa ga babban shafi

Jam'iyyar RPF mai mulkin Rwanda ta ayyana Paul Kagame a matsayin dan takararta a zaben kasar

A kasar Rwanda a yau Asabar ne jam'iyya mai mulki da aka sani da Rwandan Patriotic Front (RPF) mai mulkin kasar Rwanda ta ayyana shugaban kasar Paul Kagame a matsayin dan takararta na zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 15 ga watan Yulin wannan shekara a wani wa'adi na hudu na shekaru bakwai.

Shugaba kuma dan takara Paul Kagame
Shugaba kuma dan takara Paul Kagame AFP - TONY KARUMBA
Talla

Jam’iyyar mai mulkin wannan kasa ta nunar cewa ta zabe shi ne, ba tare da adawa ba, a yayin taron da suka kamala a yau Asabar.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame REUTERS - JEAN BIZIMANA

Paul Kamage, mai shekaru 66, ya mulki kasar Rwanda karkashin ikon kama karya tun a tsakiyar shekarun 1990, kuma ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a wannan kasa, a zabukan 2003, 2010 da 2017.

 Frank Habineza na jam'iyyar adawa a kasar Rwanda
Frank Habineza na jam'iyyar adawa a kasar Rwanda © AP

Daya daga cikin 'yan takararsa a zaben shugaban kasa shi ne shugaban jam'iyyar adawa ta Green Party, Frank Habineza.

Dan majalisar mai shekaru 47, dan majalisar ya samu kashi 0.45 ne kacal na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa na 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.