Isa ga babban shafi

Victoire Ingabire, ‘yar adawar shugaba Kagame ba ta da izinin tsayawa takarar shugaban kasa

A yau Laraba ne wata kotu a Rwanda ta yi watsi da bukatar dawo da hakkin farar hula ga Victoire Ingabire, ‘yar adawar shugaba Paul Kagame,a haka matakin ya hana ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a yi a ranar 15 ga watan Yuli.

Victoire Ingabire a zaman kotu
Victoire Ingabire a zaman kotu AFP PHOTO/Steve Terrill
Talla

Victoire Ingabire 'yar adawa mai shekaru 55, wacce ba za ta iya daukaka kara kan wannan hukuncin ba tsawon shekaru biyu, a haka kotu ta soke hakkinta bayan da aka yanke mata hukuncin daurin shekaru 15 a shekara ta 2013.

Victoire Ingabire da sanar da wannan hukunci ta bayyana  shi a matsayin keta hakkin bil Adama, ta na mai cewa "ba za ta  yarda da wannan hukunci ba, ta na mai bayyana shi da siyasa.

Victoire Ingabire Umuhoza, 'yar adawa ga Shugaba Paul Kagame
Victoire Ingabire Umuhoza, 'yar adawa ga Shugaba Paul Kagame AFP/Bertrand Guay

Wannan mata ta dawo kasar Rwanda a watan Janairun 2010 bayan ta yi shekaru 16 a kasar Netherlands,Victoire Ingabire 'yar asalin Hutu ta shafe yawancin lokacinta a gidan yari.

An kama ta tare da zargin ta da musanta gaskiyar kisan kiyashin, bayan da ta nemi a ranar 16 ga watan Janairun 2010, a ziyarar da ta kai wurin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Kigali, cewa su ma a hukunta wadanda suka aikata laifukan bangaren Hutu.

An sake ta ne a watan Satumbar 2018 a wani bangare na afuwar da shugaban kasar ya yi wa fursunoni sama da 2,000.

 Victoire Ingabire bayan ta fito daga gidan yari
Victoire Ingabire bayan ta fito daga gidan yari Cyril NDEGEYA / AFP

Shugabar kungiyar Dalfa Umurunzi (Development and Freedom for All) Kigali ba tare da izini ba, Victoire Ingabire ta bayyana muradinta na tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Yuli da Paul Kagame, wanda ta zarge shi musamman da tauye 'yancin fadin albarkacin baki, don murkushe 'yan adawa. da kuma yin watsi da mafi yawan talakawa.

Shugaban kasar Rwanda  Paul Kagame
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame AFP - TONY KARUMBA

A cikin wata sanarwar manema labarai da aka buga a shafukan sada zumunta, ta bayyana "bacin ran ta", da kuma jadadda aniyarta na kare  manufofinta, a karshe ta na mai cewa "Na kuduri aniyar ci gaba da fafutukar tabbatar da dimokuradiyya ta gaskiya a Rwanda, tare da bayar da shawarar mutunta 'yancin dan Adam da bin doka da oda."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.