Kasashe 45 ne ke tsananin bukatar taimakon abinci daga ketare-MDD
Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya tace kasashen Africa 33 ne ke tsananin bukatar abinci daga kasashen ketare ko kuma hukumomin bada agaji na duniya.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta FAO ta ce jimilla kasashen duniya 45 ke da wannan bukata cikin gaggawa cikin su 33 daga nahiyar Africa, sai 9 daga yankin Asia da guda 2 daga yankin Latin Amurka da Karebiya sai guda1 a yankin turai.
Rahoton da hukumar ta fitar yace wannan bukata ta samo asali ne sakamakon tashin hankali da ake fama da shi a yankin gabashin Asia, da kuma yammaci da gabashin Africa, lamarin da ke ta’azzara karancin abinci.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake samun karuwar kwararar hamada a wasu kasashen kudancin Africa.
Rahoton ya ci gaba da cewa noma da fitar da alkama ya ragu matuka a Afrika ta kudu, kasar da ke kan gaba wajen fitar da alkamar a nahiyar Afrika, a sakamakon tsananin zafi da sauyin yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu