Isa ga babban shafi

Kasashen yammaci sun yi tir da nasarar Putin a zaben Rasha

Shugabanni da sauran abokan huldar da ke dasawa da shugaban Rasha Vladmir Putin, sun gaggauta taya shi murnar a nasarar zaben da yayi, sai dai daukacin shugabannin kasashen yammacin Turai sun yi tir da zaben, wanda suka bayyana a matsayin haramtacce.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

Cikin sakon taya murnar da ta aike wa Putin, China ta yi alkawarin cigaba da ririta kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninta da Rasha, gami da zurfafa kawancen da suka kulla kan muhimman lamurra.

Shi kuwa tsohon shugaban kasar ta Rasha Dimitri Medvedev ya aike da nasa sakon na taya Putin murnar sake lashe zaben da yayi ne ta shafin Telegram tun ma kafin fitar da sakamakon nasarar tazarcen da shugaban ya sake yi a hukumance.

“ Yayanmu yayi nasara, wanda kuma hakan muhimmin batu ne da zai amfani duniya” a cewar shugaban Venezuela Nicolas Maduro.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da ya shafe sama da shekara guda ya na fafata yaki da makocin nasa, watsi yayi da sakamakon zaben na Rasha, inda ya kara da cewar duniya ta san ko waye Vladimir Putin, wanda mulki ya  rufewa idanu  ta yadda zai iya aikata komai da cigaba da zama kan shugabanci har abada.

A nasa bangaren babban jami’in diflomasiyar kungiyar tarayyar turai EU Josep Borrell cewa yayi ko shakka babu abinda zaben Rasha ya kunsa face illa da nuna tsantsar karfin iko da kuma yi wa masu kada kuri’a barazana.

Faransa ma dai ra’ayi guda ta bayyana da EU kan zaben, inda ta kara da jinjinawa dimbin ‘yan Rasha da suka bayyana adawarsu da shugabancin Vladimir Putin; yayin da ministan harkokin wajen Birtaniya David Cameron ya ce haramtacccen zaben da ya gudana a Rasha ya bayyana rashin zabin da ‘yan kasar suka tsinci kansu ciki, ballantana mai a kai ga batun bai wa jami’an kasa da kasa damar sa ido kan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.