Isa ga babban shafi

Likitoci sun yi nasarar dasawa fitaccen mawakin Najeriya Idris Abdulkarim koda

An samu nasarar yiwa fitaccen mawakin nan na Najeriya, Eedris Abdulkareem dashen koda, kamar yadda abokin mawakin myke Pam ya tabbatar.

Fitaccen mawakin Najeriya Idris Abdulkarim kenan
Fitaccen mawakin Najeriya Idris Abdulkarim kenan © daily post
Talla

Rahotanni daga kasar na cewa, matar mawakin ce ta bashi kodarta guda domin a dasa masa.

A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Facebook, Myke Pam ya lura cewa an yi aikin tiyatar ne da sanyin safiyar Litinin.

Mawakin ya yi fice ne ta cikin wasu daga cikin wakokin da ya yi, irin su Jaga-jaga da Mr Lecturer. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.