An haramtawa Will Smith halartar bikin gasar Oscar na tsawon shekaru 10
An dakatar da fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hollywood Will Smith daga halartar bukukuwan gasar Oscar na tsawon shekaru 10.
Wallafawa ranar:
Matakin ya zo ne makwanni biyu bayan da jarumin ya bai wa duniya mamaki ta hanyar yin katsalandan a tsakiyar bikin ba da kyautukan na Oscar inda ya mari jarumin barkwanci Chris Rock, saboda rahar da yayi kan matarsa wadda ke fama da rashin lafiyar da ta karkadar mata da gashin kanta.
Shugabannin gasar karrama jaruman fina-finan ta Oscar kusan dubu 10 ne suka yi taro da safiyar jiya Juma'a don tattaunawa kan marin da Will Smith ya shararawa jarumin barkwanci Chris Rock.
Sai dai hukuncin na su bai soke kyautar gwarzon gasar ta Oscar da Smith ya samu a watan da ya gabata ba, saboda fim din da ya kasance tauraro a cikinsa wato "King Richard”.
Zalika ba a hana Will Smith tsayawa takarar gasar ta Oscar a nan gaba ba.
A cikin taƙaitaccen bayani kan hukuncin da ya hau kansa, Smith ya bayyana amincewa tare da mutunta matakin da aka dauka a kansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu