Isa ga babban shafi

Burna Boy ya doke wasu manyan mawakan duniya a Amurka

Shahrarren mawakin zamani dan Najeriya Burna Boy da wata mawakiyar ‘yan kasar Kamaru mai suna Libianca, sun yi nasarar lashe babbar kyautar gasar da ake kira BET wadda a wannan karo aka gudanar a birnin Los Angeles na Amurka ranar lahadin da ta gabata. 

Burna Boy
Burna Boy Amy Sussman / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / Getty Images via AFP
Talla

Burna Boy wanda cikakken sunansa shi ne Damini Ogulu. ya lashe babbar kyauta wato ‘‘Best International Act’’ award ne bayan ya doke manyan mawaka irinsu Aya Nakamura daga Faransa, Ella Mai, da Stormzy da kuma Ayra Starr dukanninsu daga Birtaniya. 

Daga lokacin da aka fara bayar da kyautar a 2018, kusan a kullum mawaka ‘yan Najeriya ne ke lashe ta, domin kuwa  Davido shi ne zakaran farko da ya lashe gasar, daga nan sai Burna Boy da ya ci gaba da samun nasarar har sau 4 a jere, wato a shekara ta 2019, 2020 da kuma 2021 sai kuma wadda aka kammala a ranar lahadin da ta gabata. 

Ita kuwa mawakiya Libianca Kenzon Kinboum Fonji daga Kamaru, ta yi  nasarar lashe kyauta ta biyu mafi girma a wannan gasa wato ‘’Best New International’’ award, ta hanyar doke wani mawaki dan Najeriya mai suna Asake.  

Masoya wadannan mawaka dai sun yi sharhi sosai ta kafafen sada zumunta bayan fitar sakamakon, yayin da wasu ke yaba wa Burna Boy da kuma Libianca game da daukakar da suka samu, wasu kuwa na ganin cewa tauraron Asake, ya gaza haskakawa a gasar ne saboda mafi yawan wakokinsa yana rera su ne a cikin harshen Yarbanci zalla. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.