Isa ga babban shafi

Fitattun Hollywood sun bada gudummawar tallafa wa marasa karfin cikinsu

Jaruman masana’antar Hollywood a kasar Amurka na ci gaba da gudanar da  yajin aikin da suka shiga  tun ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata, al'amarin da ya tsaida dukkanin ayyukan  kamfanonin nishadin  masana'antar. 

Arnold Schwarzenegger, trsohon gwamnan California kuma fitatacccen jarumin Hollywood.
Arnold Schwarzenegger, trsohon gwamnan California kuma fitatacccen jarumin Hollywood. AFP
Talla

Da dama daga cikin su ne yau da gobe ke ci gaba da fuskantar tsananin matsin rayuwa ta fannin tattalin ariziki sakamakon wannnaan yaajin aiki. 

Taurarin jarumai da dama ne, irinsu Leonardo DiCaprio,  Arnold Schwarzenegger,  Julia Roberts ko kuma  Nicole Kidman, su ka bayar da tallafi mai tsoka ga asusun taimakon jinkai  na SAG-AFTRA, da kungiyar kwadagon jaruman ta kafa. 

Asusun tallafin dai  ya yi armashin da ya kai ga tara kimanin dalar Amurka  miliyan 15,  tun bayan fara yajin aikin zuwa yau. 

 Dwayne Johnson, da aka fi sani da  The Rock ne, ya kaddamar da soma armasa asusun. Shahararen jarumin da aka sani da matukar kirki, da kuma son taimaka wa marasa galihu, shi kadai ya bai wa gidauniyar   ta  SAG-AFTRA tallafin dalar Amurka miliyan daya. 

Sauran taurarin da suka hada da, Leonardo DiCaprio, Nicole Kidman, Oprah Winfrey, Matt Damon, Ryan Reynolds, a jimilce  sun bada tallafin  dala miliyan guda. 

Za a dai iya cewa, kungiyar jaruman na matukar bukatar tallafin gaggawa,   da ya linka sama da sau talatin, idan aka kwatanta shi da lokacin da komai ke tafiya daidai. 

 George Clooney da Meryl Streep su ma, sun saka hannuwa aljihu domin bunkasa gidauniyar, tare da yin kira ga sauran taurarin da su ma  su tallafa wa masu karamin karfin dake cikinsu. 

A yayin da take tsokaci, jaruma Meryl Streep ta bukaci wadanda Allah ya daukaka a sana’ar da su taimaka wa na kasa da su, inda ta ke   cewa tana tuna ranar da ta ke a matsain mai aiki bada lemu da barasa, da kuma lokacin da ta ke bin dogon layin neman aiki a kamfanonin shirya fina finai,  in ji  jarumar da ta sha sabe kambayen shahararun jarumai na Oscars  har guda uku. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.