Isa ga babban shafi

Qatar na karbar bakuncin gasar kyau ta rakuma

Yayin da wasan kwallon kafa ke daukar hankalin duniya a Qatar, kasar ta kuma karbi bakuncin gasar kyawawan wasu nau’ikan dabbobi.

Mangiah Ghufran, rakumar da ta lashe gasar kyawu na rakuma a gasar da ta gudana a Qata
Mangiah Ghufran, rakumar da ta lashe gasar kyawu na rakuma a gasar da ta gudana a Qata © Siasat
Talla

Daidai lokacin da akasarin idanun mutane ke kan gasar cin kofin duniya ta Fifa, rakuma daga ko'ina cikin yankin gulf na fafatawa a bikin kyawun kyawawa na rakuma Mzayen a Ash-Shahaniyah.

“Tsarin dai kusan daidai yake da gasar cin kofin duniya ta FIFA, muma muna shirya gasar rakuma kyawawa ta duniya,” in ji shugaban hukumar shirya gasar Hamad Jaber Al Athba.

Rakuma cikin dagawa suna tauna hakoransu ke yin jerin gwano, yayin da ‘yan kwallo da alkalai ke ci gaba da mahawara kan wadanda suka kece raini.

Gasar da ake yi tsakanin rakuma tana da zafi ga nau'o'i daban-daban musamman bisa tsarin shekaru da kuma shiga.

Ana tantance bakaken rakuma gwargwadon girman jiki da kai da kuma wurin da kunnuwa suke,” in ji Al Athba. "Amma rakumi irin na Maghateer, muna duba girmansu da daidaiton gabobi, sai kunnuwa su yi kasa, kada su mike tsaye, baya ga yadda baki ke lankwashewa."

Don guje wa ha’inci da kuma gano wa ko an yi wa rakuman tiyata ta gyaran jiki, kwamitin likitoci na bincikar dabbobin kafin ya ba su damar shiga gasar kyawawan.

Gabanin bayyana wanda ya lashe gasar ta wannan rana, ana shan nonon sauran rakuma mata, kuma mai wanda ya fi samar da ruwan nonon, ana bashi kyautar Riyal din Qatar 20,000 kimanin dala 5,500.

Wani dan kasar Saudiyya wanda rakumansa suka lashe kyautar tagulla da zinare a gasar, Mohanna Ibrahim Al Anazi, ya ji dadi bayan samun kyautarsa.

"Ba zan iya kwatanta yadda nake ji ba, domin wannan macen tana da masu bibiyarta kamar masu kallon gasar cin kofin duniya, kamar Real Madrid ko Manchester United," in ji shi. "kuma masu sha’awar kallon gasar suna nuna jin dadin su kamar yadda magoya bayan kwallon kafa suke yi a duk lokacin da kungiyarsu ta samu nasara."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.