Isa ga babban shafi

Fitacciyar mawakiyar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Tshala Muana ta rasu

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na cikin makoki. A yau asabar aka sanar da mutuwar daya daga cikin gishikan ya’na ta a fagen waka da kida na zamani da aka sani da Tshala Muana da akasarin yan kasar ke kira “Mamu Nationale”.

Tshala Muana
Tshala Muana © rfi
Talla

‘Yar asalin yankin kasai na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo kuma marubuciyar wakoki da dama, Tshala Muana ta rasu tana da shekaru 64 a duniya,na yi mata  lakabi “Mamu Nationale” ta rasu ne da sanyin safiyar yau asabar 10 ga watan Disamba a birnin Kinshasa.

Wasu ‘yan uwan ​​Tshala Muana ne suka tabbatar da wannan bayanin, Claude Mashala daya daga cikin lmasu zama da marigayiyar ta hanyar wani sako da aka wallafa a shafinsa na Facebook ya tabbatar da haka.

A sakon da ya rubuta a shafinsa,ana iya karanta cewa “Da sanyin safiyar yau, Ubangiji nagari ya yanke shawarar karbar ran Mamu Tshala Muana.

 A shekarar 1997, bayan shekaru ashirin a birnin Paris, Tshala Muana ta shiga harkokin siyasa, tare da samun goyan bayan  shugaba Laurent-Désiré Kabila. Ta kafa kungiyar REFECO kungiyar da ke tallafawa matan Congo.

Daga 2000 zuwa 2002, ta kasance a matsayin memba na majalisar da ke bayar da shawarwari mai zaman kanta.

Daga nan ta zama shugabar kungiyar mata ta PPRD4 (Jam’iyyar Jama’a ta Reconstruction and Democracy), jam’iyyar siyasa da Shugaba Joseph Kabila ya kafa a shekarar 2002, matsayin da har yanzu take rike da shi kafin rasuwar ta.

A shekarar 2011, ta sha kaye a zaben ‘yan majalisar dokoki a mazabar Kananga, zaben dai a cewarta an tafka magudi.

Tun lokacin da ta shiga harkokin siyasa, Tshala Muana ta kasance ƙwararriyar mawaƙiyar  siyasa da na kishin ƙasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.