Isa ga babban shafi

Duniyar mawaka na jimamin mutuwar Tina Turner

Fitacciyar mawakiyar, Tina Turner, wacce ta shahara a duniyar waka kamar The Best da What's Love Got To Do with It, ta rasu tana da shekaru 83 a duniya.

Mawakiya Tina Turner
Mawakiya Tina Turner © Gie Knaeps/Getty Images
Talla

Kamar yadda rahotanni ke cewa, Turner ta sha fama da matsalolin rashin lafiya da dama a cikin 'yan shekarun nan, da suka danganci ciwon daji, mutuwar barin jiki da kuma matsalar koda.

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoto game da rayuwar marigayiyar

Ta yi suna tare da mijinta mai suna Ike a cikin shekarun 1960 tare a wasu wakokinta irin su Proud Mary da River Deep, Mountain High.

Ta rabu da mijin nata a shekarar 1978 sakamakon cin zarafi da take fuskanta daga wurin sa, inda ta ci gaba da samun nasara a duniyar mawaka a shekarun 1980.

An haife ta a Tennessee, inda ta fara shahara sannu a hankali daga cikin mawakan da suka yi fice a wancan lokaci.

Mawaka masu tasowa a wancan lokaci da suka hada da Beyonce, Janet Jackson, Janelle Monae da kuma Rihanna, sun tasirantu da baiwarta.

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Michael Kuduson

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.