Isa ga babban shafi
Madagascar

Kotun Madagascar ta daure mutane 5 tsawon shekaru kan yunkurin juyin mulki

Wata kotu a Madagascar ta yanke wa wasu mutane biyar da suka hada da Faransawa biyu hukuncin daurin shekarun da suka kama daga 5 zuwa 20 a gidan Yari, bisa samun su da laifin kitsa yunkurin juyin mulki a kasar.

Hoton gudumar, Kotu ko kuma ta Alkali manta sabo.
Hoton gudumar, Kotu ko kuma ta Alkali manta sabo. © REUTERS/Andrew Kelly/Illustration
Talla

Mutanen da aka yankewa hukuncin dai na cikin mutane 20 da ake zargi da yunkurin kashe shugaba Andry Rajoelina a cikin watan Yuli.

A ranar Juma’ar da ta gabata wata kotu ta samu biyar daga cikin mutanen da laifukan shirya kisa, neman dagula harkokin tsaron kasar, da kuma kafa gungun  miyagu masu aikata laifuka.

Biyu daga cikinsu, Paul Rafanoharana mai takardar zama Bafaranshe da matarsa ​​Voahangy Andrianandrianina kuma, an same su da karin laifuka na mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, abinda ya sanya aka yakewa mijin hukuncin daurin shekaru 20, maidakinsa kuma daurin shekaru 5, tare da aiki mai wuyar gaske.

Shi kuwa tsohon sojan Faransa Kanal Philippe Francois hukuncin daurin shekaru 10 aka yanke masa, tsohuwar abokiyar kasuwancinsa Aina Razafindrakoto ta sami shekaru biyar. A yayin da aka yanke wa tsohon Firayim Minista Victor Ramahatra hukuncin daurin shekaru biyar na talala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.