Isa ga babban shafi

Uganda: An kwantar da dalibai 150 a asibiti saboda gubar abinci

Akalla dalibai 150 ne daga makarantar sakandare ta Nakanyonyi da ke gundumar Mukono a kasar Uganda, aka garzaya da su asibitoci daban-daban bisa zargin cin gubar abinci.

Galibi daliban da ke bangaren kwana na makarantar ne abin ya fi shafa.
Galibi daliban da ke bangaren kwana na makarantar ne abin ya fi shafa. © reuters
Talla

A cewar mataimakin kakakin ‘yan sandan birnin Kampala, Luke Owoyesigyire, daliban sun fara korafin ciwon ciki ne bayan sun ci abincin dare ranar Laraba.

"Bayan shan shayi a ranar Alhamis, alamun sun karu, inda suka fara jin ciwon ciki akai-akai," in ji Owoyesigire.

Ya ce an garzaya da wadanda abin ya shafa asibitin Naggalama da babban asibitin Mukono domin basu kulawar gaggawa.

“An dauki samfuri daga jikin wadanda abin ya shafa tuni aka aka aika da su zuwa dakin gwaje-gwaje na gwamnati da ke Wandegeya domin a tantance ainihin musabbabin matsalar yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin,” inji Owoyesigyire.

An bayyana cewa, ana iya sanya gubar a cikin tankin makarantar da aka yi amfani da ruwa wajen girka abincin daliban.

Galibi daliban da ke bangaren kwana na makarantar ne abin ya fi shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.