Isa ga babban shafi

Uganda ta kama jagoran mayakan da suka kashe masu yawon shakatawa a kasarta

Hukumomin Uganda sun tabbatar da kama jagoran ‘yan bindigar da ake zargi da kashe wasu ‘yan kasashen waje, da ke yawon shakatawa tare da mai yi musu jagora a watan jiya, a wani wurin shakatawa.

Wasu daga cikin sojojin Uganda da ke yaki da mayakan ADF a kan iyakar kasashen biyu.
Wasu daga cikin sojojin Uganda da ke yaki da mayakan ADF a kan iyakar kasashen biyu. REUTERS - Kenny Katombe
Talla

Rundunar sojojin kasar ta ce,wanda suka kama shi ne kadai ya tsira daga farmakin da suka kai cikin daren Talata kan mayakan kungiyar ADF din, wanda rundunar ta ce ta kashe shida daga cikin wadanda suka aikata ta'asar.

Masu yawon shakatawar da suka hada da dan kasar Burtaniya David Barlow da mai dakinsa ‘yar Afirka ta Kudu Celia tare da mai jagoransu dan kasar Uganda Eric Ayai, an kashe su ne a wani hari da aka kai ranar 17 ga watan Oktoba da ya gabata, yayin da suke wajen shakatawa na tunawa da Sarauniya Elizabeth.

Mataimakin kakakin rundunar sojojin Uganda Deo Akiiki, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, sun samu nasarar kashe dukkanin mayakan ADF da suka ketaro daga Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo don kashe masu yawon shakatawan, in banda jagoransu da shima suka samu nasarar kamawa kuma ake kula da shi a wani kebantatcen wuri kafin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Ya kuma ce, sun samu wanda ake zargin da wasu daga cikin kayayyakin masu yawon shakatawan da suka kashe da kuma katin shedar mai yi musu jagora.

Majo Janar Dick Olum da ke jagorantar rundunar Uganda da ta ke yaki da mayakan ADF a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Congo, ya ce sun kuma sami nasarar kashe wasu mambobin kungiyar 6 a wani hari na daban da suka kai a ranar Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.