Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Zuma ya sauke ministan kudin Afrika ta Kudu

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya sallami ministan kudin kasar Pravin Gordhan a wani garambawul da ya yi wa majalisar ministocinsa, in da ya maye gurbinsa da ministan cikin gida Malusi Gigaba.

Pravin Gordhan da shugaba Zuma ya sauke daga mukamin ministan Kudin Afrika ta Kudu
Pravin Gordhan da shugaba Zuma ya sauke daga mukamin ministan Kudin Afrika ta Kudu REUTERS/Sumaya Hisham
Talla

Shugaban ya kuma nada Sfiso Buthelezi a matsayin mataimakin ministan kudi don maye gurbin Mcebisi Jonas.

Shugaba Zuma na ci gaba da shan matsayin lambar sauka daga mukaminsa bayan ya kira Gordhan da ya dawo gida daga London a farkon wannan makon.

Da dama daga cikin al’ummar Afrika ta Kudu na kallon Gordhan a matsayin babbar garkuwar yaki da cin hanci a kasar, kuma kiran da Zuma ya yi masa daga London ya rage darajar kudin kasar na Rand da kashi 5 cikin 100.

Ana zargin shugaba Zuma da halasta kudaden haramun a kasar, abin da ya jefa shi cikin tsaka mai wuya.

Kazalika Garambawul din ya yi wa ministocin nasa ya shafi ma’aikatun makamashi da ‘yan Sanda da kuma yawon bude.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.