Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

‘Yan gudun hijiran Sudan ta Kudu na cikin tsaka mai-wuya

Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban ‘yan gudun hijirar Sudan ta kudu na zama a Kahrtoum ba tare da muhalli ba, sakamakon rusa matsugunan su da ‘yan Sandan Sudan suka yi.

Sansanin da wasu daga cikin 'yan gudun hijiran Sudan ta kudu ke rayuwa
Sansanin da wasu daga cikin 'yan gudun hijiran Sudan ta kudu ke rayuwa Thomson Reuters Foundation/Stefanie Glinski
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta yi zargin cewar ‘yan Sandan na ci gaba da rusa matsugunin ‘yan gudun hijirar ko kuma sauya musu matsuguni ba tare da sanarwa ba.

Akalla ‘yan kasar Sudan ta kudu 450,000 suka tsallaka cikin Sudan domin kaucewa yakin basasar da aka samu a cikin kasar tun daga shekarar 2013.

Sudan ta ce akalla ‘yan kasar Sudan ta kudu miliyan daya da rabi suka samu mafaka cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.