Isa ga babban shafi

Togo na jagorantar taro kan amfani da takin zamani da inganta kasar noma

Gwamnatin kasar Togo ta shirya wani taron kasashen duniya a kan amfani da takin zamani wajen noma da kuma ingantar kasar noman a yankin Afirka ta Yamma. 

Kasashen Afrika na fuskantar matsalar takin zamani duk da yadda kaso mai yawa na al'ummomin karkararsu suka dogara da noma.
Kasashen Afrika na fuskantar matsalar takin zamani duk da yadda kaso mai yawa na al'ummomin karkararsu suka dogara da noma. AFP - FADEL SENNA
Talla

Taron na zuwa ne bayan an dauki dogon lokaci masana aikin noma na gudanar da bincike akan tasirin takin zamani da kuma amfani da shi, kamar yadda aka kaddamar a Jamhuriyar Nijar a shekara ta 2021, wanda ya samar da ci gaban noma a fadin kasar. 

Ana saran taron na yau ya sake duba hanyoyin ci gaban fasahar noma da kuma tabbatar da dorewar samar da takin domin inganta gonaki da kuma samar da sabbin dabarun zamani ga manoma. 

Taron na rana guda na samun taimakon Bankin Duniya da Cibiyar Bunkasa takin zamani na duniya. 

Daga cikin mahalarta taron harda shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.