Isa ga babban shafi

Afirka ta Kudu ta bukaci Isra'ila ta tsagaita buda wuta a yakin da ta ke yi a Gaza

Afirka ta Kudu ta bukaci ganin Isra'ila ta tsagaita bude wuta a yankin Gaza a fadan da ta ke gwabzawa da Hamas, a yayin da ta yi zargin zalunci  a irin matakan da ta dauka.

Ministar huldar kasa da kasa ta Afirka ta kudu Naledi Pandor
Ministar huldar kasa da kasa ta Afirka ta kudu Naledi Pandor Jacques Nelles.jpg
Talla

Ministar huldar kasa da kasa Naledi Pandor ce ta kasar ta bayyana hakan a yayin da ta ke jawabi ga majalisa dokokin kasar, kwana guda bayan kasar ta janye jakadunta daga Isra'ila

Ba za mu iya lamuntar wannan ba, domin zalunci ne karara. Dole ne mu yi kira da a tsagaita wuta a yanzu a matsayinmu na 'yan majalisar Afirka ta Kudu," in ji ministan Afirka ta Kudu Naledi Pandor.

A ranar 7 ga watan Nuwamba ne aka cika wata guda da mayakan Hamas suka kai wani hari mafi muni a tarihin Isra'ila, inda suka kashe mutane 1,400, galibi fararen hula, tare da yin garkuwa da wasu 239, a cewar jami'an Isra'ila.

A yayin da Isra’ila ta mayar da martani kan harin da Hamaz ta kai mata wanda ya kashe mutane sama da dubu 10 a Gaza, kuma kashi 40 na wadanda suka mutu kananan yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.