Isa ga babban shafi

Rasha ta dawo da yan kasar ta dake hannun kurdawan Syria gida

Kurdawan dake rike da yankin arewa maso gabashin kasar Syria a yau asabar  sun mika yara marayu  20 ga wata tawagar hukumomin Rasha domin mayar da su gida.

Distribution de l'aide alimentaire dans le camp de déplacés d'Idlib en Syrie.
Distribution de l'aide alimentaire dans le camp de déplacés d'Idlib en Syrie. REUTERS - KHALIL ASHAWI
Talla

A watan Maris na shekara ta 2019 ne mayakan Kurdawa suka sanar da murkushe kungiyar Isil da ta kafa gwamnatin ta a karkashin ikon Khalifa a Syria, yayin da murkushe kungiyar ta IS  a lokacin ne ya baiwa kurdawan damar mayar da dimbin mata yan kasashen waje kasashen su na assali tare da rakiyyar yaran da suka haifa a lokacin da ake tsare da su a sansanoni da dama.

Photo prise dans le camp d'al-Hol géré par les Kurdes, qui abrite des proches présumés de combattants du groupe État islamique (EI), dans le gouvernorat de Hasakeh, dans le nord-est de la Syrie, le 3 mars 2021.
Photo prise dans le camp d'al-Hol géré par les Kurdes, qui abrite des proches présumés de combattants du groupe État islamique (EI), dans le gouvernorat de Hasakeh, dans le nord-est de la Syrie, le 3 mars 2021. AFP - DELIL SOULEIMAN

Majiya daga yankin na tabbatar da cewa a dan tsakanin nan kusan 'yan kasar Rasha 200 ne aka mayar da su kasar su tare da hadin guiwar hukukumomin na Rasha.

Rasha da kasar Uzbekistan na daga cikin kasashen da yanzu haka ke da hulda da Kurdawa dangane da wannan shiri na mayar da marayu dama yan kasar zuwa gida daga kasar Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.