Isa ga babban shafi

Mutane 8 suka mutu a wani harin Taliban a Kabul dake Afghanistan

An samu fashewar abubuwa har sau biyu a birnin Kabul na kasar Afghanistan, yayin da dakarun kasar ke tafka kazamin fada da mayakan Taliban a birnin Lashkar Gah da ke kundancin kasar.

Harin kungiyar Taliban daf da birnin Kabul
Harin kungiyar Taliban daf da birnin Kabul AP - Rahmat Gul
Talla

Daya daga cikin fashewar ta faru ne a kusa da gidan ministan tsaron kasar, kafin daga bisani a ji karar musayar wuta tsakanin dakarun gwamnati da kuma maharan.

Birnin kaboul na kasar  Afghanistan
Birnin kaboul na kasar Afghanistan REUTERS - OMAR SOBHANI

Wata majiya daga rundunar sojam Afghanistan na cewa Ministan tsaron kasar na cikin koshin lafiya,banda haka sojojin dake kare lafiyar sa sun yi nasarar murkushe maharani ga baki daya.

Hukumomin kasar yanzu haka na kira ga jama’a mazauna yankunan da ake gwabza fada da su gujewa wadanan yankuna cikin gaggawa.

Kungiyar Taliban ta dau alhakin harin  da aka kai da safiyar yau laraba a wata unguwa dake da cikkaken tsaro,harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8 a Kabul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.