Ma'aikata bakin haure 50 ne suka mutu a Qatar
Hukumar kwadago ta Duniya(OIT) ta fitar da wani rahoto dake nuni cewa akalla ma’aikata 50 bakin haure dake aiki a wurarren gine-ginen filayen wasani dangane da gasar cin kofin Duniya suka mutu, da dama suka samu munanan raunika .
Wallafawa ranar:
An dai jima ana kalon kamfanoni dake aiki da wadanan ma’aikata bakin haure a Qatar a matsayin masu keta hakokkin bil adama.
A wanan rahoto da hukumar ta fitar,ta na mai bayyana cewa akasarin mutanen da suka rasa rayukan su a shekara ta 2020 sun mutu ne bayan hatsari wurin aikin gini, ko hatsarin mota, kazalika ma’aikata 506 da akasarin su bakin haure ne suka samu rauni, a shekara ta 2020 mutane 37.600 ne suka samu kananan raunika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu